Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu guda hudu a jihar Kano. Hakan ya biyo wata kudiri ce da majalisar jihar ta mika wa gwamnan jihar bayan amincewa da asake fasalin masautun jihar Kano din.
Tuni dai har gwamna Ganduje ya rattaba hannu a akai ta zama doka.
Dokar ya kirkiro sabbin manyan masarautu har guda hudu da suka hada da masarautar Karaye dake da kananan hukumomi 8 a karkashinta, Masarautar Bichi dake da kananan hukumomi 9, Masarautar Rano dake da kananan hukumomi 10 sai kuma masarautar Gaya dake da kananan hukumomi 9 dakuma masarautar kano dake da kananan hukumomi 8 ita ma.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ne zai zama shugaban majalisar sarakunan Kano din.
A jawabin sa, gwamna Ganduje ya ce Kirkiro wadannan masarautu zasu taimakwa wa mutane sannan ci gaba ne akai wa mutane kusa da su. Ya ci wannan babban abin ci gaba da aka samu dole a yi murna da shi saboda ya yiwu ne a wannan babban wata na Ramadana.
Discussion about this post