GA DADI GA BAN HAUSHI: Marafa ya jinjina wa hukuncin Kotun Koli

0

Sanata Kabiru Marafa da ke wakiltar Shiyyar Zamfara ta Tsakiya, ya bayyana hukuncin da Kotun Koli ta yanke na korar APC daga zabukan jihar, cewa babbar nasara ce ga dimokradiyya.

Marafa wanda dan jam’iyyar APC ne, ya ce wannan nasara cewa ga jihar Zamfara da al’ummar ta da ma kasa baki daya.

Ya yi wannan jawabi ne a yau Juma’a a Abuja, bayan Kotun Koli ta zartas da hukuncin cewa ta kori APC kuma ta soke dukkan zabukan gwamna, majalisun tarayya da na sanatoci da majalisar dokokin jiha wanda APC ta shiga.

Marafa ya sha fama da gwamna Yari, wanda shi gwamnan ya rike sai jam’iyyar APC a Zamfara, ya kasance sai abin da yaga dama ya rika yi da jam’iyyar.

Kabiru Marafa ya ci gaba da cewa, “Komai daren dadewa wata rana duk inda aka binne gaskiya, to wata rana sai ta bayyana, kuma sai ta dusashe hasken karya”.

Don haka ya ce Kotun Koli ta yi hukunci mai nuna cewa nasara ce ga kasar nan da dimokradiyya baki daya.

‘Wannan zai sa a rika bin ka’idar dokar kasa da kuma yin abin da ya dace a yi.

Marafa ya kara da cewa hukuncin ya kara nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba ya shiga kuma ba ya yin katsalandan a harkokin shari’a.

Ya kuma gode wa fannin shari’a, musamman alkalan Kotun Daukaka Kara, irin su Mai Shari’a Tom Yakubu da sauran.

Sannan ya yaba wa INEC da har ta nuna ba sani ba sabo wajen hana Zamfara shiga zabe.

Ya yaba wa Kotun Koli da ya ce ta zamar wa al’umma wajen kai kukan su ga kotu, inda sun tabbata za a share musu hawayen su.

Share.

game da Author