Kamfanin Facebook ya rufe shafin sadarwar wani kmfanin kasar Israila bayan an gano cewa ya rika watsa bayanan farfaganda da yarfen siyasa a kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a lokacin kamfen na shugaban kasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press, ya ruwaito cewa kamfanin na kasar Israila mai suna Arcimedes, ya rika yada farfagandar sakonnin goyon baya ga Shugaba Muhammadu Buhari.
A lokacin da Arcjimedes ke watsa sakonnin goyon baya a kan Buhari, gefe daya kuma ya na yayata sakonni na farfagandar siyasa da yarfe a kan Atiku Abubakar.
Rahoton dai ya nuna wata cibiyar binciken kafofin sadarwar zamani na soshiyal midiya, mai suna Atlantic Council’s Digital Forensic Research Lab ce ta bankado wasu shafuka da aka yi wa Atiku yarfen siyasa, sakonnin da Facebook ya gano cewa duk kage ne da kirkira.
Tambarin shafin an nuno Atiku ne da siffa irin ta ‘boss’ na cikin fim dim ‘Star Wars’, mamuguncin nan mai suna Darth Vader, ya na rike da wani sam-bodi da aka rubuta: “Ku Zabe Mu, Mu Kara Lalata Najeriya.”
Taken kamfen din Atiku Abubakar dai shi ne “Ku Zabe Mu, Mu Sake Farfado da Najeriya.”
Rahoton ya ci gaba da nuna cewa Archimedes ya rika kwarzanta Buhari da gwarzanta shi a matsayin wani “zaki kakkarfa.”
An kuma gano Archimedes ya rika tsokanar wasu shafukan Facebook na magoya bayan Atiku, inda ya rika dunbuza musu farfagandar goyon bayan Buhari, duk kuwa da cewa ba su nemi ya tura musu ba.
An yi kiyasin cewa bayanan sun isa ga kimanin mutane miliyan 2,800,000.
An kuma gano cewa kamfanin ya kashe naira milyan 288.4 wajen watsa sakonnin kage da yarfe da farfaganda ga jama’a.
Discussion about this post