Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kasa reshen jihar Edo (EFCC) ta kama wasu ma’aikatan hukumar bada Katin shaidar rigakafin zazzabin shawara guda hudu.
EFCC ta kama wadannan ma’aikata rana 14 ga watan Mayu bayan matar da suka damfara ta kai kara.
Matar ta bayyana cewa ma’aikatan hukumar sun bukaci ta biya Naira 10,000 kafin su bata katin shaidar rigakafin zazzabin shawara.
Da lokacin tafiya ya yi sai ma’aikatan filin jirgi na Murtala Muhammed dake Legas suka gano cewa katin da ke hannun wannan mata na jabu ne.
Nan da nan matar ta sake biyan Naira 2,000 a filin jirgin domin samun ainihin katin.
Bayan matar ta shigar da kara sai EFCC ta aika da ma’aikatan ta biyu zuwa hukumar.
Ma’aikatan sun je hukumar ne da suna cewa suna bukatan katin inda ma’aikatan hukumar suka bukaci kowanen su ya biya Naira 7,000.
Bayan ma’aikatan EFCC sun biya wadannan kudade kuma sun karbi katin su sai sauran ma’aikatan EFCC suka kama su.
EFCC ta ce za ta kai wadannan mutane kotu bayan ta kammala bincike.