Hukumar EFCC ta daukaka karar da ta shigar da Robert Azibaola, dan ‘uwan Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, wanda Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta sallama daga zargin wawure dala miliyan 40.
Kakakin Yada Labarai na EFCC Tony Orilede ne ya bayyana haka a cikin wata takardar da ya aiko wa PREMIUM TIMES, inda ya bayyana korar karar wadda Mai Shari’a Nnambi Dimgba ya yi a matsayin abin takaici matuka.
TIRKA-TIRKA
EFCC ta ce lauyoyin ta za su yi nazarin hukuncin da Babban Mai Shari’a Nnamdi Dimgba ya zartas, wanda ya ce EFCC ta kasa gabatar da shaida, sannan kuma za ta dauki matakin daukaka kara.
“EFCC ta nuna damuwa, duk da irin shaidun da ta gabatar wa kotu, amma Mai Shari’a Dimgba ya ce tilas sai EFCC ta nuna kai-tsaye yadda wanda ta ke zargin ya karbi kudaden, sannan kuma ta nuna yadda aka yi ta san cewa kudaden na harkalla ne.” Haka EFCC ta bayyana.
Idan ba a manta ba, ranar Litinin PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Mai Shari’a Dimgba ya kori karar a bisa abin da ya kira rashin kwararan hujjojin da kotu za ta iya kama Azibaola da laifi.
Da ya ke yanke hukunci a ranar Litinin din, Mai Shari’a Dimgba ya ce duk da an dade tsawon lokacin ana tafka wannan shari’a, EFCC ta kasa gabatar wa kotu kwararan hujojin da za su iya tabbatar da cewa Azibaola ya ci kudaden.
Ya ce kamata ya yi mai gabatar da kara ya gabatar masa da tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro, Sambo Dasuki, a matsayin mai bayar da shaida.
“Tunda mai gabatar da kara ya kasa gabatar da shaida daga ofishin Mashawarci a Fannin Tsaro, babu wata hujjar da ke tabbatar da an bayar da kudi, kuma wanda ake zargi ya karba din.
HUKUNCIN MAI SHARI’A
“EFCC da mai gabatar da kara sun nuna azarbabin damuwa da shari’ar, fiye ma da wanda ake zargin an yi wa lafin (Gwamnatin Tarayya kenan).
“Sannan kuma mai gabatar da kara ya kasa tabbatar da hujjoji sahihai wadanda za a ce ga hujja ba wai zargi ba, a dukkan caje-caje guda biyun da suke yi wa wanda ake kara.”
“Don haka na sallami wanda ake kara, ya tashi ya tafi, an wanke shi, ba shi da laifi.” Inji Mai Shari’a Dimgba.
Idan za a iya tunawa, EFCC ta kama Azibaola, dan’uwan Jonathan, suka maka shi kotu tare da matar sa Stella da kamfanin sa.
Discussion about this post