Duk wanda ya ce zai rika sauraran majalisar dattawa, kwakwalwar sa ko zata buga – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ba kasafai bane mutum zai damu da sauraren muhawaran ‘yan majalisar dattawan Najeriya.

El-Rufai ya ce tatsuniyoyi kawai suke shirgawa a majalisar da idan ka ce zaka saurare su tabbas kwakwalwar ka zai iya buga wa.

Gwamnan ya yi wadannan maganganu ne bayan ganawa da yayi da shugaban Kasa a fadar gwamnati a Abuja.

Manema labarai sun nemi yayi bayani kan cewa da wasu sanatoci suka yi wai titin Kaduna zuwa Abuja ya fi kowani titi a kasar nan zama mai hadari.

El-Rufai ya musata wannan magana inda ya ce shi dai bai san da wani ma’auni sanatocin suka yi nasu gwajin ba domin jami’an tsaro suna aiki matuka wajen ganin an kau da wadannan miyagun mutane a wannan hanya.

” Titin Kaduna zuwa Abuja yayi kyau yanzu, jami’an tsaro na aiki ba dare ba rana a wannan titi, abinda zan iya fadi kenan. Amma wasu sun taru a wani zaure suna fadin abinda ba haka ba.

Baya ga nan El-Rufai ya fayyace maganganun da yayi game da yadda za’a iya karya loggon ubangida a jihar Legas.

” Maganan da nayi ban ambaci sunan wani ba domin tambaya ne aka yi min game da ubangida a siyasa. Na fede musu biri daga kai har wutsiya yadda na ragargaza ‘yan siyasan ubangida a jihar Kaduna, na yi musu ritayar karfi da yaji.

” Amma wasu sun je sun lauya maganar. Abin da na sani shine na yi wannan magana kuma bana tsoron wani don na fadi haka. Duk wanda ma ya dauka da shi nake toh mishi can, ni babu abinda ya sha min kai.

Share.

game da Author