Babu wata kasa a duniya da zata cigaba har sai ‘ya’yanta suna bin doka kuma sun yadda bin dokar shine babban dalilinsu na zama a karkashin kulawar gwanati.
Rashin bin doka yana mayar da alqarya ta zama ‘Primitive society’ ma’ana nahiyar da babu cigaba sai kauyenci da jahilci da zalunci.

Duk kasar da ta wayi-gari babu aiki da doka a cikinta, to babu shakka tana cikin matsala ta shugabanci da tsaro da kuma mulkin mallaka.
Hakika, a cikin bangarori na gwamnati (Organs of government), kotu itace take da alakin hukunci idan aka yiwa doka karantsaye. Ma’ana, kotu tana daukar matsayi irin na alqalin wasa (referee) a cikin filin wasa.
Duk lokacin da aka wayi-gari kotu bata da ikon yanke hukunci a saurareta, gaskiya an shiga uku. Saboda haka ne ma ake kiranta da hukuma mai zaman kanta (Independent judiciary).
Ita wannan kalma ta ‘Independence’ ana so ne ta zama a bayyane tana aiki, ba wai kawai a baki ba.
Ta yaya hakan zai kasance?
Wajibi ne masu mulki da wadanda ake mulka su yi biyayya ga kotu da hukuncinta na adalci saboda a jaddada ‘supremacy’ dinta a aikatance.
Idan aka samu gyara a kotunan Najeriya (Judiciary), da hukumomi masu tursasawa a bi doka (Law enforcement agencies), babu shakka su kansu talakawa zasu yi biyayya musamman idan gwamnatin tasu tana da ‘legitimacy’.
An dade a Najeriya ana maganar matsayin kotu da hukumar zabe. Idan ance duk hukumomi ne masu zaman kansu, to ya kamata mu ga suna da cikakken ‘Administrative Autonomy’ wanda zai basu dama su gudanar da ayyukansu.
A ina matsalar take?
Dole sai an daina yin ‘Winner-takes-all politics’ a Najeriya. Ma’ana, duk wanda yaci zabe ya mallaki komai na kasa ko jihar da yake mulka idan gwauna ne.
Matsalar tana da alaqa da hanyoyin samar da shugabanci da samun kudin hukumomin. Misali, duk sanda aka ce shugaban kasa shi yake da wuka da nama wajen samar da shugabanci da kudi na hukumomin, to akwai matsala babba.
Shugaban kasa ne yake mikawa majalisa sunan wanda yake so ya zama shugaban hukumar zabe ko kotun koli na kasa. Kudadensu ma daga gwamnati mai ci suke.
To yaushe wadanda aka basu aikin yi zasu kafircewa ubangidansu?
Abun yana da bukatar nazari kwarai da gaske, dole ne sai wadannan hukumomi ya zama suna da hanyoyin samar da shugabancinsu da kuma samun wata hanya da kudinsu zai dinga zuwa hannunsu.
Allah ya shiryar damu.