Duk da matsalar tsaro, Barno ta fi Kebbi, Ebonyi da Ekiti tara kudin shiga

0

Duk da matsanacin fama da hare-haren Boko Haram da ke a Jihar Barno, bayanan kididddiga sun nuna cewa jihar ta fi Kebbi, Ebonyi da Ekiti tara kudaden shiga da haraji.

Wannan rahoton na kunshe a cikin bayanan rahoton Tara Kudaden Shiga na Jihohi a karshen shekarar 2018.

Cikin makon da ya gabata ne Hukumar Kudiddigar Bayanai (NBS), ta buga wannan bayani a shafin ta na intanet.

Wadannan kudade ne da jiha ke tarawa ta ke samu daga harajin da ake biya daban-daban a cikin jiha.

Cikin 2018, jihar Barno ta tara naira bilyan 6.52. Yobe naira bilyan 4.38, Adamawa naira bilyan 6.20, sai Ekiti naira bilyan 6.47. Ebonyi kuma naira bilyan 6.14.

Jihar Taraba ta tara naira bilyan 5.97, ita kuma Kebbi ta tara harajin naira bilyan 4.88.

Legas ta tara harajin naira bilyan 382.16, wato kwatankawacin harajin da jihohi 29 suka tara kenan.

Jihar Ribas ta tara harajin naira bilyan 112.78, sai Ogun naira bilyan 84.55. Ita kuwa Delta naira bilyan 58.44.

Jihar Kano ta tara naira bilyan 44.11 a cikin 2018, yayin da Akwa Ibom naira bilyan 24.21.

Share.

game da Author