Shirin inganta kiwon lafiyar yara kanana (CDGP) dake karkashin kungiyar ‘UK Department for International Development (DFID)’ ya tallafa wa rayukan mata masu ciki 52,393 a jihar Zamfara.
Jami’in shirin Tanko Muhammed ya bayyana haka a taron tattauna tsara hanyoyin rayar da shirye tallafa wa mutanen karkara da DFID ke yi a garin Gusau ranar Laraba.
Mohammed yace shirin CDGP ya tallafa wa mata masu ciki a kauyuka 527 dake kananan hukumomin Anka da Tsafe da Naira 4000 duk wata domin kula da ‘ya’yan su tun daga shekarar 2014 zuwa 2019.
” DFID ta fara wannan shiri ne a 2014 domin inganta kiwon lafiyar yara kanana a jihohin Jigawa da Zamfara. Sannan ana biyan mata naira 4000 duk wata domin kula da kan su.
Mohammed ya yabawa goyan bayan da suke samu daga shugabannin kananan hukumomin Tsafe da Anka wajen ganin shirin yayi nasara.
Da yake tofa albarkacin bakinsa jami’in ma’aikatar kasafin kudi na jihar Zamafar kuma jami’i a shirin CDGP Kabiru Muhammed yace DFID tare da hadin guiwar kungiya mai zaman kanta ‘Save The Child International’ sun shirya wannan taro ne domin tsaro wasu shiri don tallafawa talakawan jihar.
Discussion about this post