DAWOWAR BUHARI: Fadar Shugaban Kasa ta ragargaji masu yada ji-ta-ji-ta

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga tafiyar da yi ta radin kan sa zuwa kasar Ingila.

A sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, a yau Lahadi da misalin karfe 6:24 na yamma.

Kakakin yada labarai na Shugaba Buhari, Femi Adesina, ya fitar da wani kakkausan jawabi a yau cewa:

“Wasu kafafen soshiyal midiya ‘yan shirme da giribtu, tare da wasu ‘yan siyasa marasa mutunci da wasu dibgaggun daidaikun mutane, sun rika watsa karairayi cewa wai Shugaba Buhari ya tafi ne a kwantar da shi asibiti, kuma ba zai dawo a ranar da aka yi sanarwar dawowar ta sa ba, bayan kwana 10.”

Adesina ya ce abin na su ya ma wuce wuri, har su na kirkirar karyar cewa “likitoci sun shawarci Buhari ya kara tsayawa a kula da shi, a bangaren da ake kula da wadanda suka kusa kai gargara.”

Daga nan sai ya ce to yanzu dai Buhari ya dawo, shin wadannan marasa kunyar za su nade tabarmar kunyar su kenan? Shin za su janye karairayin da suka rika watsawa, su bayar da hakuri?

Tafiyar da Buhari ya yi ta haifar da maganganu musamman ganin yadda ba a fito an bayyana abin da zai je ya yi a Ingila ba.

Sannan kuma bai mika mulki ga mataimakin sa, Yemi Osinbajo ba kamar yadda doka ta tanadar.

Share.

game da Author