Dattijo ya roki kotu ta raba dadadden auren sa a dalilin dukan tsiya da matarsa ta ke masa

0

Wani dattijo mai suna Godwin Akinola mai shekaru 82 ya roki kotun dake Agege a jihar Legas da ta raba aurensa da matarsa Anthonia bisa yawan duka da barazanar kashe sa da ta keyi.

Akinola ya kuma roki kotun data bata tazara a ranar da za a ci gaba da shari’ar domin ‘yan uwan su su sam su sasanta su.

” Kulum Anthonia na lakada mun dukan tsiya sannan ta kan yi barazanar kashe ni.

” Na auri Anthonia akalla sama da shekaru 30 da suka wuce kuma mun haifi yaron da ke da shekaru 35 yanzu amma duk wadannan abubuwa basu hana Anthonia ci mani mutunci ba.

Akinola ya ce da ya gaji kuma ya nemi ya rabu da matarsa ta sa sai ‘yan uwansa da ‘yan uwan ta suka roke shi da kada a raba auren gashi ma duk sun tsufa.

A karshe alkalin kotun Patricia Adeyanju ta shawarci ma’auratan da su je su sasanta tsakanin su.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 22 ga watan Agusta.

Share.

game da Author