Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Batsari/Danmusa/Safana, Hon. Dayyabu Safana, ya yi matukar nuna damuwa dangane da yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane da ke faruwa a Jihar Katsina, jihar da Shugaba Muhammadu Buhari ya fito.
Kashe-kashen sun yi tsamarin da har Safana ya nemi a kafa dokar-ta-baci a wasu kananan hukumomin jihar Katsina.
Safana ya ce abin ya kai har ana bi cikin kauyukan da ya ke wakilta ana kashe mutane ana kuma kona musu dukiyoyi da gidaje.
Kashe-kashen bai tsaya a kananan hukumomin da Dayyabu ke wakilta kadai ba. ana ci gaba da samun rahotannin kashe-kashe da garkuwa da jama’a a sauran kananan hukumomi da dama na jihar.
Na baya-bayan nan shi ne garkuwa da Magajin Garin Daura da aka yi kwanaki uku da suka wuce.
An sace Musa Umar, a kofar gidan sa a Daura, lokacin da ya ke zaune a kan benci, ya na jiran lokacin sallar isha’i, ya yi sallah kafin ya shiga gida.
Musa Umar kanin Sarkin Daura ne, sirikin Buhari ne, kuma sirikin dogarin Buhari ne.
Hon. Safana ya yi wannan korafi ne a Zauren Majalisar Tarayya, inda ya nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta kai dauki a kananan hukumomin Safana/Batsari/Danmusa, inda mahara ke ci gaba da kashe mutane, garkuwa da kuma lalata dukiyoyin jama’a.
“Ba kawai su ke yi su na banka wa gidaje wuta, su saci mata da mazaje wadanda ba su da karfi, su kuma majiya karfin su bi su su karkashe. Yanzu kauyuka hudu a mazaba ta na fama da wannan tashin hankali na hare-hare.
“Sun kai wa kauyukan Massa, Alhazawa da Guzurawa hari inda suka karkashe mutane da kona gidaje da dukiyoyin su.
“Jiya-jiyan nan kuma sun je har cikin kauyen Gobirawa a Karamar Hukumar Safana, suka kashe mutane 12, suka kona gidaje da dukiyoyi.
’Yan Majalisa da dama sun yi tir da yadda ake ta yawan kashe-kashen jama’a musamman a karkara, amma hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya ta kasa yin wani hobbasa.
A kan haka ne Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya ce ya zama tilas Majalisa ta gayyaci Shugaba Buhari domin ya zo ya yi mata jawabi dangane da wannan kashe-kashen da ake ci gaba da yi.
Daga nan sai Dayyabu Safana ya nemi a gaggauta sa dokar-ta-baci a wasu kananan hukumomin Jihar Katsina.
Sannan kuma ’yan majalisar sun yi kira ga gwamnati da ta tura sojoji domin su rika taimaka wa ‘yan sanda domin a kamo maharan masu kai hare-hare.
Da dama sun goyi bayan Dayyabu Safana domin a kafa dokar-ta-baci a kananan hukumomin da abin ya fi shafa.
Ba wannan ne karon farko da aka fara yin kuka dangane da jihar Katsina ba.
Cikin watan Janairu, Gwamna Aminu Masari ya ci Katsina mamaye ta ke da masu garkuwa da mutane.
Kwanaki kadan bayan yin wannan kalami aka je har gida aka sace sirikar sa a cikin garin Katsina, aka yi garkuwa da ita tsawon sati daya kafin a kubutar da ita.
Discussion about this post