DALLA-DALLA: Dalilan Saukar Zainab Bulkachuwa Daga Alkalancin Shari’ar Atiku Da Buhari

0

Shugabar Kotun Daukaka Kasa ta Kasa, Zainab Bulkachuwa, ta janye daga shugabancin Alkalan Shari’ar Kararrakin Zaben Shugaban Kasa.

Baya ga janyewa daga shugabancin, Zainab ta kuma tsame kanta daga cikin alkalai biyar da za su yi shari’ar, wadda dan takarar shugabancin kasa a zaben 23 Ga Fabrairu, Atiku Abubakar ya shigar.

Akwai kuma wasu jam’iyyu hudu baya ga PDP da Atiku, wadanda suka maka INEC, APC da Shugaba Muhammadu Buhari a kotu, inda suke kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2019, da aka gudanar a ranar 23 Ga Fabrairu.

Atiku tare da jam’iyyar sa PDP, ya maka INEC, Buhari da jam’iyyar APC kotu, bisa zargin cewa an yi masa magudi a zaben.

Ya nemi a sake zabe kwata-kwata, bisa dalilai da tulin hujjojin da shi Atikun y ace ya ke da su, wadanda ya fara bayyana wasu, wasu kuwa sai shari’a ta yi nisa za a fara ji da ganin su.

ATIKU DA BULKACHUWA: Asali Da Dalilin Tirka-tirka

Jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar sun garzaya kotun a ranar da za ta saurari karar ta su, jim kadan bayan rantsarwa da kaddamar da alkalan su biyar, a bisa shugabancin Zainab Bukachuwa, Shugabar Kotun Daukaka Kara, kuma wadda aka ce za ta shugabanci alkalai hudu da za su yi shari’ar, sai kuma ita a cikon ta biyar.

Atiku da PDP sun ce ba su amince da Zainab Bulkachuwa a cikin alkalancin shari’ar da za a fafata ba, saboda ba za ta yi masu aldalci ba.

Atiku da PDP sun nemi sai dai Zainab ta janye, kuma ta sauka, domin “ba adalci kadai ake son a yi a shari’a ba. Ana kuma so jama’a su gamsu cewa lallai an yi adalcin.

Atiku da PDP sun gabatar da takaradar korafi mai dauke da shafuka 19, cewa ba su gamsu da Zainab Bulkahuwa a cikin alkalan ba, saboda ta na da akala ta kut-da-kut da jam’iyyar APC, wadda suke kara.

Cewa Zainab matar rikakken dan APC ce, Adamu Mohammed Bukachuwa, jigo a cikin jam’iyyar, wanda ya fito takarar sanata a jihar Bauchi kuma ya yi nasara.

Dan Zainab mai suna Aliyu Haidar dan jam’iyyar APC ne, har takarar zaben fidda-gwani na takarar gwamnan Jihar Gombe ya fito, a karkashin APC amma bai yi nasara ba.

Aliyu Haidar ya taka rawa wajen kamfen din neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

Atiku ya ce akwai Alkalai sama da 80 a Kotun Daukaka Kara, wadanda za su iya yin shugabancin shari’ar, ba lallai sai Zainab ta nada kan ta ba.

Atiku da PDP sun ce kalamin da Zainab ta furta a ranar kaddamar da Alkalan Shari’ar Kararrakin Zaben Shugaban Kasa, sun kashe musu guiwa cewa ba za su yi tsammanin aldalci daga gare ta ba.

Zainab ta furta cewa: “ Ana gudanar da zabuka a Najeriya duk bayan shekara hudu. Duk irin yadda aka gudanar da zabe mai inganci, sai an samu wadanda suka yi korafi.”

Atiku da PDP sun ce “wannan furuci da Zainab ta yi, ya nuna cewa ta rigaya ta nuna an gudanar da zaben shugaban kasa mai inganci kenan. Kuma ta nuna cewa karar da suka shigar ta na daya daga cikin irin korafe-korafen da ta ce za a yi duk kuwa da cewa zaben ya yi kyau.”

Mataimakin Sakataren Jam’iyyar PDP, Mista Agbo, wanda shi ne ya gabatar wa kotu takardar korafin, a ciki ya kara da cewa:

“ Na san Zainab a matsayin matar Hon. Adamu Mohammed Bulkachuwa, don haka ba za ta iya yanke hukuncin shari’ar nan ba, ba tare da duk wani mai hankali da tunani ya darsasa wani zargi a zuciyar a ba, ciki kuwa har da ni kai na.”

“ Na kuma san cewa tabbas dan ta na cikin ta, Aliyu Haidar Abubakar shi ma cikakken dan jam’iyyar APC ne, ya na da katin shaidar jam’iyya, kuma ya fito takarar gwamna a zaben fidda-gwani a jihar Gombe.

“ Ga ma takardun shaidun cewa Haidar ya yi takara, kuma ya yi wa wanda mu ke kara kamfen kamar, yadda fastocin da muka kwafo daga shafin sa na Facebokk suka nuna.

“Ga kuma wata shaida nan daga jaridar Daily Post online news, da ta tabbatar da cewa Aliyu Haidar ya yi takara a zaben fidda-gwanin APC na gwamnan jihar Gombe: (Sechttps://dailypost.ng/2018/09/16/gombe-2019-justicebulkachuwas-son-joins-race-succeed-dankwambo/ampl)

“ A ranar 27 Ga Okotoba, 2018 kuma jaridar Daily Post online news, ta sake buga labarin cewa: Jam’iyyar APC ta bai wa Adamu Mohammed Bukachuwa tikitin takarar Sanata, domin neman alfarma daga Shugabar Kotun Daukaka Kasa, wadda a matsayin ta na matar sa, kuma kotun ta ce za ta saurari kararrakin zabukan fidda-gwani. Kuma ga shaida nan na bayar a rubuce kamar haka:

(Seehttpszl/dailypostmg/ZOI8/]0/27/apcbauchi-stalwarts-claim-oshiomhole-gave-tuggars-ticket-appeal-courtpresidents-husband-bulkachuwa-documents/)

“ Na halarci zaman farko na alkalan shari’ar kararrakin zaben shugaban kasa, a ranar 8 Ga Mayu, 2019, inda Shugabar Kotun, Zainab Adamu Bulkachuwa ta yi wani furuci kamar haka: “Ana gudanar da zabuka a Najeriya duk bayan shekara hudu. Duk irin yadda aka gudanar da zabe mai inganci, sai an samu wadanda suka yi korafi.”

BUHARI BAI SAN DAN ZAINAB YA YI MASA KAMFEN BA – Lauya

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa cewa ba shi da masaniyar dan shugabar kotun na cikin ta, mai suna Aliyu Haidar ya taya shi kamfen a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa kafin zaben 2019.

Buhari ya ce sai ma bayan da ya karanta dalilan korafin da Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP suka shigar, inda suka nemi Zainab ta fice kuma ta sauka daga shugabancin kotun shari’ar sannan ya karanta, ya sani.

Ya kara da cewa an kuma janyo hankalin sa a kan wani labari daga wata jarida wanda Atiku da PDP suka gabatar wa kotu, wanda aka buga Aliyu Haidar din ya taya shi kamfen a wani shafin sa na Facebook.

Sai dai kuma duk da haka, lauyoyin Buhari sun shigar wa kotun rubutaccen martani ga zargin da Atuki da PDP suka yi.

Lauyan mai suna Kolawole Andrew daga ofishin Babban Lauyan Buhari, Wole Olanipekun, ya ce masu korafi sun kasa gabatar da shaidar cewa an yi musu ko an nuna musu wani son kai ko rashin adalci.

Buhari, wanda lauyoyin sa suka wakilta a kotu jiya Laraba, ciki har da manyan lauyoyi bakwai, ya kara da cewa tun da ya hau mulki bai taba tsoma baki a sha’anin hukunci ko shari’ar kowace kotu ba.

Ya kuma ce ba shi da ikon da zai ce ga wanda za a nada a cikin kwamitin alkalai masu shari’ar zaben shugaban kasa ko na gwamna ko ma wane zabe.

Daga nan sai alkalan Buhari suka nuna cewa Atiku da PDP duk ba su da wani dalilin da zai sa jikin su ya yi sanyi don kawai Shugabar Kotun Daukaka Kararrakin Zabe, Zainab Bulkachuwa na ciki.

Sun dai ci gaba da kawo hujjojin su na cewa tun da Atiku da PDP suka fara gabatar da takardun shigar da kararrakin su, Zainab ba ta taba nuna musu wani bambanci ko nuna son kai ko bangaranci ba.

RA’AYOYIN LAUYOYIN INEC DA NA APC

Ra’ayin lauyoyin Buhari ya zo daidai da na lauyoyin INEC da na jam’iyyar PDP. Dukkan su sun nuna cewa babu wani dalilin da zai sa Atiku da PDP su fara wata tashin-tashina a kan Zainab, domin ba a nuna musu son kai ko fifiko ba. Kawai su na kuka ne da tsoron abin da babu shi kwata-kwata.

Shi ma lauyan INEC, Yunus Usman, ya ce Atiku da PDP kame-kame kawai suke yi, domin dokar kasa ba ta hana don ka na auratayya da wani dan siyasa ba, shikenan ba za ka yi alkalancin zabukann siyasa ba.

Jagoran Lauyoyin APC, Lateef Fagbemi, ya ce dama PDP ta sama yi wa mutane kazafi da kulla musu tuggu, ba wannan ne karo na farko ba.

Sai dai shi kuma babban lauyan PDP, Levy Uzoukwu, ya dade shi ma ya na jaddada dalilan da ya ce su ka wajaba Zainab ta sauka, domin ita ma da kan ta ta nanata cewa alkalai su kasance babu wani dardashin wani zargin nuna son kai, bangaranci ko zargin nuna rashin adalci a kan su.

HUKUNCIN KOTU A KAN ZAINAB BULKACHUWA

Daya daga cikin alkalan kotun mai suna Peter Ige, ya karanto hukuncin kotun a madadin sauran alkalan, ya ce korafin da Atiku da PDP suka shigar zargi ne kawai a kan Zainab, cewa akwai yiwuwar za ta yi rashin adalci, amma babu inda aka ce ta yi rashin adalcin.

“Sun gina tsoron su ne kawai daga dangantakar ta da wasu masu dauke da katin shaidar wata jam’iyya.

“ Ina da yakinin cewa babu wata kwakwarar shaida da suka gabatar da za ta tabbatar da cewa Shugabar Kotun Daukaka Kara za ta yi musu rashin adalci.

“ Don kawai ta na matar dan jam’iyyar APC, kuma uwar dan jam’iyyar APC, ba wadatattun hujjoji ba ne da za a ce ta sauka kuma ta tsame kan ta daga cikin alkalan da za su yi hukuncin wannan shari’a. Saboda iyalan ta ba su cikin wadanda ake kara.” Inji Babban Mai Shar’a Ige.

Daga nan sai y ace wannan korafi ba shi da wata madogara, kuma ya yi watsi da shi.

SAUKAR BULKACHUWA DAGA ALKALANCIN ATIKU DA BUHARI

Bayan alkalai sun gama yanke hukunci, sai Zainab ta jajirce ta ce duk da haka gara dai ta janye, saboda wadansu dalilai na radin kan ta kawai.

“Na sauka ne kawai don dalilai na kashin kai na.”

Share.

game da Author