Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa manyan asibitoci da suka hada da asibitocin koyarwa na jami’o’I za su fara aiki yadda ya kamata a kasar nan idan gwamnati ta inganta asibitocin jihohi da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko.
Adewole ya fadi haka ne a zauren majalisar dattawa.
Ya ce bisa ga yadda tsarin yake, gwamnati ta gina manyan asibitoci ne domin duba cututtukan da suka gagari asibitocin jihohi da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko.
” Kamata yayi asibitocin jihohi da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko su duba kashi 70 bisa 100 na marasa lafiya, inda ya gagagre su sai a garzayo manyan asibitoci. Amma yanzu ba haka bane kanannan asibitocin duk sun mutu kowa manyan yake zuwa.
Sai dai kuma hakan ba shine ke faruwa ba a Najeriya domin rashin inganta wadannan ya sa mutane na yin tururuwa zuwa manyan asibiti wanda a dalilin haka ya sa manyan asibitocin ke fama da matsaloli da suka hada da rashin ma’aikata, rashin kayan aiki, cikowan mutane da sauran su.
MAFITA
Adewole yace gwamnati za ta yi nasarar cimma burinta na samar da kiwon lafiya na gari ga kowa da kowa cikin sauki ne idan ta inganta asibitocin jihohi da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko.
Gwamnati za ta yi nasara a wannan fannin ne idan ta;
1. Hana ‘yan siyasa gina asibitocin da ba a bukata; Akwai asibitocin jihohi 17 da cibiyoyin kiwon lafiya sama da 100 a kasar nan wanda yau an wayi gari kadan daga cikinsu ne ke aiki yadda ya kamata. Hakan ya sa mutane ke tururuwa zuwa manyan asibitoci 22 da ake dasu.
2. Karkato da hankalin gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi wajen daukar nauyin kula da aibitocin jihohi da cibiyoyin kiwon lafiya
3. Bude asusu da gwamnatin tarayya, na jihohi da kananan hukumomi za su iya yi wa asibitocin jihohi da cibiyoyin kiwon lafiya tanadi.
4. Karo ma’aikata da samar da ingantattun kayan aiki wa asibitoci.
A karshe ministan ya ce gwamnati ta dauki kwararrun ma’aiaktan da za su gudanar da bincike domin gano hanyoyin inganta kiwon lafiya da suka fi dacewa a kasar nan.
Discussion about this post