Sakamakon bincike da aka yi a kasa Najeriya don gano dalilan da ya sa aure ki yi wa matasa wuya, ya nuna cewa mafi yawan matasa a wannan zamani da muke ciki sun gwamace su ci gaba da zama a matsayin gwauraye mai makon su yi aure.
A gani su hakan ya fiye musu sannan babu ruwan su da fadawa cikin matsaloli da suke ganin idan sun yi aure za su fada.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya tattauna da wasu gauraye dake zama a yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja inda suka bayyana wasu dalilian da ya sa aure yake neman ya gagari musamman maza a wannan lokaci da muke ciki.
Emmanuel Chime yace daya daga cikin matsalolin dake hana maza aure shine yawan tula kudin da ake narkarwa a wasu al’adu a lokacin da mutum ya nemi ya auri ‘yar su.
” A gani na bai kamata mutum ya dauki shekaru da dama yana tara kudi ba sannan ace wai a lokaci guda ya kashe su kawai wai don al’ada na wata kabila ba.
Sunday Aboki cewa yayi shi ana shi ganin akwai wasu irin al’adu da wasu ke da shi da kan sa maza su gudu idan za su auri ‘ya daga irin wadannan yaruka. Namiji sai ya kasa yin auren domin ba zai iya jure wa wadannan al’adu ba.
Joy Micheal kuwa kokawa tayi da irin tilasta wa saurayi da ake yi da sai ya biya wasu kudade na musamman da tsula masa kudin sadaki, Idan ba zai iya ba sai kaga ya gudu abin shi.
” Kiri-Kiri ina gani ina son saurayina yana so na amma haka muka rabu domin irin tsawwala masa kudin sadaki dana al’ada da iyaye na suka yi masa. Ba zai iya ba sannan na yi iya kokarina amma babu yadda na iya. Ina kuka yana hawaye haka ina gani yayi tafiyar sa.
Duk ire-Irenn wadannan matsaloli ne ke takura saurayi da budurwa da har sai ka ga aure bai yiwu ba duk da suna son juna.
Na’omi Danjuma kira ta yi ga iyaye da su hakura su dan rika sassauta wa maza ko don irin halin da kae ciki na rashin kudi. Sannan kuma wasu abubuwan na al’ada yakice su wasu ma a rika watsi dasu.
A bincike da PREMIUM TIMES HAUSA ta yi, akwai masoya da dama da a halin yanzu sun koma suna zama ne tare wuri daya ba tare da an daura musu aure ba. Da dama daga cikin su ma har ‘ya’ya suke dashi. Bincike ya nuna cewa kusan wadannan dalilai da muka ambato a baya sune makasudin abin da ya sa haka ya ke faruwa.
Bayan haka akwai wadanda kuma ba zaman tare za suyi ba, sukan amincewa junan su ne mace ta haifi da daya da saurayin ta, shi kenan ba sai sun yi aure ba, a hakan ma zai iya tafiyar sa. ita dai burin ta tana da da.
Wasu daga cikain dalilan da ya sa aure ke wahala ga maza da mata sun hada da:
1 – Tsananin Talauci – Maza da dama kan koka kan rashin aikin yi ko sana’a a matsayin babban dalilin da ke hana su yin aure.
2 – Rashin gaskiya a tsakanin masoya – Anan sai kaga ba namijin ba ba macen ba. Duk su biyun sai surika shirga wa junan su karerayin da daga baya idan suka gane juna sai zantakewa ya gagara har su rabu.
3 – Banbancin Al’ada – A dalilin banbance-banbancen al’adu wasu da dama cikin maza sukan gudu ko kuma su fasa auren saboda ba za su iya jure wani yanki na al’adan mace ba ko kuma na bangaren saurayin nata.
4 – Addini – Banbancin Addini – Akan samu matsala matuka idan addininin masoya bai zo daya ba. Za kaga wasu suna soyayya da juna amma a dalilin rashin kasancewa a addini daya sai kaga abin daga karshe ya watse. Sannan kuma ba wai don basu son juna ba.
5 – Yaudara – Da dama masoya kan dade suna soyayya amma duk a cikin yaudara. Wannan yafi aukuwa ga mata. Sai kaga mace na son saurayinta tsakani da Allah amma ashe yana yi mata yaudara ce. Babu gaskiya a abinda ya kaisbhi gare ta. Sai bayan tafiya ta yi tafiya sai kaga duk abin ya watse an rabu ana ta Alla- Ya-Isa.
6 – Wayewa da tambadewa – Yawewa da ya iske mutane yanzu ya ruguza tarbiyya da zamantakewa cikin amana da ake yi ada. Yanzu shaye-shaye, da tambadewa ya sa kafin mace ta ankara ta gama zama abin tausayi. Abubuwan da ada sai an yi aure ne ake iya samun shi a jikin mace yanzu ya zama gashinan sai yadda kayi da shi duk da sunan wayewa.