Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar ya nuna cewa akalla mata 311,000 ne ke rasa rayukan su a duniya a dalilin kamuwa da cutar dajin dake kama al’aurar mace.
Bayanai sun nuna cewa mace kan kamu da cutar dajin dake kama al’aurar ta ne a dalilin saduwa da maza daban daban, kamuwa da cutar kanjamau, kamuwa da cutar sani da sauran su.
Cutar ya fi kama mata musamman masu shekaru 15 zuwa 49
Likitoci sun bayyana cewa zuwa asibiti domin yin gwaji da yin allurar rigakafi na daga cikin hanyoyin da ke sa a tsira daga kamuwa da cutar.
A kwanakin baya ne Kungiyar likitoci mai suna ‘American Cancer Society (ACS) ta gano hanyar yin gwajin jini domin gano cutar dajin dake kama mahaifan mace da wuri.
Likitocin sun bayyana cewa ana iya gano wannan cuta ce ta hanyar yin gwajin jinin da amfani da sinadarin ‘CA-125’.
Bisa ga bayanan likitocin sun ce sun gudanar da wannan bincike ne domin kawar da matsalar rashin gane cutar da wuri.
” Cutar dajin dake kama mahaifa cuta ce dake yawan kama mata sannan da dama basu sani sai cutar ta mamaye jikin mace.
Likitocin sun kuma bayyana cewa sinadarin ‘CA-125’ na taimakawa wajen kawar da wasu matsalolin da ake kamuwa da su a lokacin da mace ke da ciki, kaban ciki, laulayin haila, Hepatitis da sauran su.