CIKON KUDIN PARIS CLUB: Za a sheka wa jihohi ruwan biliyoyin nairori 649

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kwanan nan za ta raba wa jihohi sauran cikin kudin Paris Club har naira bilyan 649.434 da suka yi saura.

Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, a jiya Alhamis, yayin da ta ke wa manema labarai bayani, a taron ‘yan jaridu da ta shirya.

Wannan adadi dai bai kai ma naira bilyan 694.560 ba da Babban Bankin Tarayya, CBN ya biya cikin watan Maris, 2019.

An ce bambancin canjin musayar kudade ne ya kawo wannan gibi na sama da naira milyan arba’in.

Zainab ta ce nan ba da dadewa ba za a fara raba wa jihohi kudaden, a matsayin kashin karshe na kudaden Paris Club da aka sha ba su a baya.

FITA DAGA MATSIN TATTALIN ARZIKI

Minista Zainab ta ce wannan tsari na bai wa jihohi kudaden Paris Club, ya samu nasara gagarima wajen cicciba kasar nan ta fita daga matsin tattalin arziki da ta yi fama da shi.

An gudanar da tsarin ne a karkashin Shirin Farfado da Tattalin Arziki a karkashin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Zainab ta kara da cewa sakamakon nasarar wannan shiri, a yanzu Najeriya na kan hanyar dorewa a kan ingantaccen tattalin arziki.

Sai dai kuma ta nuna rashin jin dadi da kuma damuwa ganin yadda sauran bangarori ba su samar wa kasar nan kudaden shiga, kamar fannin harkar man fetur.

Ta ce hakan na kawo cikas wajen kasa aiwatar da muhimman ayyuka a fannin lafiya, ilmi da gina ababen inganta rayuwar jama’.

Ta ce duk da haka Najeriya ta yi hobbasan kara yawan asusun ajiyar ta na kasashen waje daga dala bilyan 28.361 a 2015, zuwa dala bilyan 44.69 a cikin Maris, 2019.

Hakan inji ta ya taimaka farashin musayar kudaden waje bai sake yin tashin-gwauro-zabo ba.

Share.

game da Author