Cikin wata uku Najeriya ta tara naira biliyan 289 daga haraji

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta tara naira biliyan 289 daga karbar harajin jiki-magayi, wanda aka fi sani da ‘Value Added Tax’ (VAT) a cikin watanni uku.

Wadannan kudaden ta ce an tara su a cikin watanni uku na farkon shekarar 2019, wato daga Janairu zuwa Maris.

Haka dai hukumar NBS ta buga a shafin ta na intanet, inda ta fitar da Rahoton Sashen Karbar Harajin Jiki-magayi (VAT) na watanni ukun farkon shekara ta 2019.

VAT harajin jiki-magayi ne da ake dora wa farashin kaya wasu kudade kashi 5 bisa 100 kudin da za rika na adadin kayan da aka saya ko aka sayar.

Wadannan kudade sun kunshi adadin hakkin da gwamnatin tarayya ke so a biya a matsayin haraji tun daga lokacin da ake hada kayan, dafa su, kera su ko sarrafa su, daukar su a kai kasuwa, har zuwa wanda zai saya ya ci ko ya yi amfani da kayan.

Rahoton ya nuna cewa wannan adadin makudan kudade ba su ma kai yawan wadanda aka tara ba a shekaru ukun karshen sharakar 2018 ba.

Sannan kuma rahoton ya kuma nuna cewa naira bilyan 298.01 aka tara a dai watanni ukun karshen 2018, ba kamar naira bilyan 289.04 da aka tara a shekaru ukun farkon 2019 ba.

Masana’antu masu kera kayayyaki ko sarrafawa sun samar da harajin naira bilyan 31.42, sai kuma bangaren ayyukan kwararru nay au da kullum da aka tatsi naira bilyan 24.31 daga gare su.

An tatsi naira biliyan 14.92 daga ‘yan kasuwa da manyan ’yan tireda masu saye sayarwa, duk a cikin wadannan watanni uku na farkon shekarar 2019.

Share.

game da Author