TAMBAYA: Shin matafiyin da ya samu magariba da Issha suka cimmai a hanya, baiyi su ba sai da ya shigo gida bayan haka. Shin zai yi Issha Kasaru ne ko kuwa zai cika. Na ga wasu na yi wa Issha kasaru. Ina rokon malam yayi min cikakken bayani don abin yana rudani.
AMSA: Alhamdu-lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.
Matafiyin da Sallah ta same sa a cikin tafiya zai yita a matsayin kasaru, Kuma idan a gida ne zai yita Matsayin ta gida, wato raka’a hudu. Matafiyi na da halaye a cikin tafiyarsa kamar haka:
1) idan matafiyi ya fara tafiyarsa sai lokacin Sallah yayi kuma ya na kan tafiyarsa, to zai yi kasarun Sallar sa ne. Kuma kasaru zai ramata idan bai yita ba har lokacin ta ya wuce a cikin halin tafiya.
2) Idan lokacin Sallah yayi matafiyi yana gida bai fara tafiyarsa ba kuma baiyi Sallah ba, sai bayan ya fara tafiya sannan ya tsaya don Sallah, to zai yi kasarun Sallar sa ne, matukar lokacin wannan Sallar bai fita ba. Sannan kasarun ne akansa koda lokacin ta yawuce.
3) Amma idan lokacin Sallar ya fita tun yana gida, to zai rama Sallah cikakkiya, wato raka’a hudu. Domin lokacin ta ya sameshi kuma ya wuce yana gida.
4) Idan Sallah ta sami matafiye a kan hanyar sa ta dawowa gida, Amma bai sallaceta ba har sai da ya dawo gida. A Nan za’a ayi la’akari da karewan lokacin Sallan ne. Kamar haka:
a) Idan lokacin Sallan ya wuce kafin ya shiga anguwarsu, to lokacin ta yawuce yana halin tafiya, sabo da haka zai ramata a Sallar kasaru.
b) Amma idan lokacin da ya Isa anguwarsu a kwai sauran lokacinta, sannan bai sallaceta ba, shi kenan ta zama Sallar gida, domin karshen lokacinta ya sameshi a gida.
Musulmai su ji tsoron Allah, su kiyaye, matukar a kwai sauran lokacin Sallah mutum ya Isa gida, to wannan Sallar ta zamo Sallar gida ba ta kasaru ba.
Mutukar mutum na son ya sallaceta Sallar kasaru, to ya yita kafin shiga anguwarsu.
Allah shi ne mafi sani.
Allah ya tsare Mana imaninmu da mutuncinmu. Amin .