Buhari ya umarci ministoci su ci gaba da aiki zuwa ranar 28 ga watan Mayu

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministoci da su ci gaba da aiki har sai ranar 28 ga watan Mayu wato ranar Talata mai zuwa.

Ranar Laraba mai zuwa ne za a rantsar da sabuwar gwamnati a kasar nan.

Buhari ya kara da cewa kowa ya mika takardar kammala aiki ga sakataren gwamnatin Tarayya.

” Yau Laraba ne rana ta karshe da za mu yi irin wannan taro da ku. Koya mika takardar kammala aiki a ofishin sakataren gwamnati tarayya.

A karshe ya gode wa ministocin bisa kokari da aiki tukuru da sukayi wajen ci gaban Najeriya.

Share.

game da Author