Buhari ya tattabar da shugabancin ’yan sanda ga Sujeto Janar Adamu

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da shugabancin rundunar ‘yan sandan kasar nan a kan Sufeto Janar Adamu Mohammed.

Kafin tabbatar da shi a jiya Alhamis, Adamu ya na mysayin Shugaban Riko ne, tun bayan nada shi da aka yi a lokacin da tsohon Sufeto Janar Ibrahim Idris ya yi ritaya.

An tabbatar masa da jagorancin ne a jiya Alhamis, a lokacin da Hukumar Gudanarwar ’Yan Sanda ke taro a fadar shugaban kasa, a karkashin jagorancin Shugaba Buhari.

Sabon Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ne ya yi wannan sanarwa a lokacin da ya ke hira da manema labarai bayan gama taron a fadar shugaban kasa.

Fayemi yace an tabbatar da shi biyo bayann duba rakod na muhimman ayyukan da ya gudanar tun daga ranar 15 Ga Janairu, 2019 da aka nada shi.

Ya ce an gamsu da kokarin sa da kuma maida hankalin sa kan aiki da gogewa da kwarewar ayyukan sa a cikin gida da wajen Najeriya, shi ya sa aka tabbatar masa da jagorancin jami’an tsaro na ‘yan sanda din.

Adamu ya zama shugaban ‘yan sanda a daidai lokacin da jami’an tsaro ke fuskantar babbar matsalar garkuwa da jama’a da kuma munanan hare-haren ‘yan bindiga da satar shanu a Arewa.

Share.

game da Author