Buhari ya tashi zuwa Umrah

0

Fadar shugaban kasa ta sanar cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tashi zuwa kasar Saudiyya domin amsa gayyatar sarkin Saudiyya da yayi masa.

Sarki Salman Bin Abdulaziz ya gayyaci Buhari ya ziyarci kasar domin yin Umrah da kuma ganawa da shi.

Buhari zai dawo kasa Najeriya ranar Talata 21 ga watan Mayu.

Share.

game da Author