Wasu ’yan bindiga da aka kyautata zaton Boko Haram ne, sun tare wani jerin gwanon motoci kusa da kauyen Molai.
Molai kauye ne da ke kusa da Maiduguri, babban birnin Jihar Barno.
An ce lokacin da aka kai wa jerin gwanon motocin hari, sojoji ne ke rakiyar su, amma hakan bai hana Boko Haram afka musu ba.
An ce maharan tun daga Damboa suka yi takakka har bayan garin Maiduguri, sannan suka fara afka wa matafiya a kusa da kauyen Molai.
Dama kauyen Molai ya sha fama da hare-haren Boko Haram jita-jifa.
Mazauna yankin sun ce tun karfe 6:30 na yamma suka fara kai harin lokacin da ake ta kokarin fara buda-baki.
Wani mai suna Bulama Aji da aka kai harin kan idon sa, ya ce maharan suna da yawan gaske.
“Su na da yawan gaske, kuma duk a cikin motoci suke. Ba wanda ya yi tsammanin cewa mahara ne, har sai da aka kusa shiga Maiduguri. Ina mamakin shin ina sojoji suke ne, har wadannan dandazon mahara suka kai wa jerin gwanon motocin su matafiya hari?
“Sai kawai mu ka ga daya daga cikin motocin ta zura a guje, ta banki motar sojojin da ke rakiyar mu. Sai kawai bam ya tashi.
“To daga nan fa sai sauran mahara da ke kan wasu motoci da yawa suka fara harbin fasinjoji lokacin kuma kowa ya arce, ya kama gaban sa a guje.
“Daga nan kuma suka shiga kauyen Molai, suka rika banka wa gidaje wuta.”
Aji ya tabbatar da cewa ba za a rasa wadanda suka mutu da yawa ba, musamman lokacin da bam din ya tashi.