Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji, sun kashe daya, wasu sun bace

0

Boko Haram sun sake kai wani hari a sansanin sojojin Najeriya a Jihar Barno, suka kashe soja daya, wasu suka ji raunuka, sannan kuma ba a san inda wasu suke ba.

Mahara na Boko Haram sun kutsa cikin sansanin da ke cikin Karamar Hukumar Gubio, da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Lahadi, kamar yadda majiyar PREMIUM TIMES ta shaida.

Sun kai farmaki a kan sansanin sojojin Najeriya na Birgade ta 5 da Bataliyar 159, suka kashe soja daya wasu kuma suka ji rauni.

Wasu sojoji shida da suka bace kuma har zuwa ranar Talata da dare, kwana biyu bayan kai harin, babu labarin su. Haka dai majiyar ta tabbatar.

Amma kuma majiyar ta ce sojoji sun yi kokarin karar mahara na Boko Haram din. Tun kafin su kai ga kara yi musu mummunar barna.

Sojoji sun kashe dan Boko Haram daya, kuma sun kwaci bindigogi daga Boko Haram din.

Har yau dai da Sojojin Najeriya bas u fitar da sanarwa a kan harin ba, kuma PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin su Sagir Musa yau Laraba da safe, amma bai amsa kira ba, kuma bai kira daga bisani ba.

Majiyar sojoji da ta tabbatar da harin kuma ta ce ba ta da iznin yin magana kuma ta nemi jarida ta sakaya sunan ta.

An yi wannan hari ne kwanaki uku bayan manoman yankin Karamar Hukumar Gubio sun yi kukan cewa sojoji su kara masu lokacin komawa gida a kullum daga gonakin su.

An dai kafa dokar cewa kowa ya koma gida daga gonar sa kafin karfe 4:00 na yamma, wanda hakan ya janyo ana kama duk wanda ya wuce lokacin bai koma gida ba.

Wannan ya sa sojojin da ke yankin suka maida dokar komawa gida akan manoman zuwa karfe 5:30 na yamma.

Sai dai kuma ba a sani ba ko dokar da a ka sassauta din ce ta yi sanadiyar samun damar da Boko Haram suka yi har suka kai hari a yankin a kan sansanin sojojin.

Share.

game da Author