A halin da ake ciki Boko Haram sun diran wa kauyen Shuwa da ke karamar hukumar Madagali, jihar Adamawa cikin wannan dare na Alhamis.
Wani mazaunin kauyen mai suna Abawu Kefas ya ce mutanen garin duk sun arce sun kyale wa Boko Haram garin.
” Wannan hari da Boko Harm suka kawo cikin dare ya sa mutanen garin Michika duk sun fice daga gidajen su domin tsoron kada su iske su.
” Wani dan banga da ke aiki da jami’an tsaro a wanna yanki ya shaida mana cewa Boko Harm sun ciccinna wa shaguna da gidajen mutane wuta sannan sun dibi na diba.