BOKO HARAM: Najeriya na bukatar tallafi domin gyara Sansanonin Gudun Hijira –Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tallafi daga Majalisar Dinkin Duniya zai taimaka matukar gaske wajen gyara mummunar barnar da Boko Haram suka yi wa Najeriya.

Haka Buhari ya shaida wa Shugabar Majalaisar Dinkin Duniya, Majalisi na 73, Maria Garces yau Talata a Abuja.

“Irin halin kuncin da mazauna sansanonin masu gudun hijira ke ciki a kasar nan, ya yi muni kwarai da gaske. Akalla mu na da kananan yara milyan daya a sansanoni wadanda ba su ma san iyayen su ba, kuma ba su san inda suka fito ba.”

Buhari ya kuma shaida wa Garces cewa irin yadda yaki da Boko Haram ya lalata kayayyakin inganta rayuwa, musamman a Arewa maso Gabas, abin ya yi muni kwarai da gaske.

“Sun karya gadoji, sun banka bama-bamai a makarantu, asibitoci, masallatai, coci-coci, da sauran gine-gine. Duk za mu gyara wadannan, sannan kuma mu na bukarar duk irin tallafin da za mu iya samu daga gare ku.”

Dangane da yiwuwar farfado da Tafkin Chadi ta hanyar jawo ruwa daga Kogin Congo, Buhari ya ce sauyin yanayi ya yi wa yankinn illa sosai.

“Akalla mutane milyan 30 ne kafewar Tafkin Chadi ta gurgunta, kuma rabin wadannan mutanen duk ‘yan Najeriya ne.

Shugabar ta yaba wa Najeriya ganin yadda ta ke kokarin shiga dukkan harkokin Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya.

“Najeriya na taimakawa kwarai da dakaru wajen samar da zaman lafiya a sassan Afrika.” Inji ta.

Ta kuma yaba da shugabancin da Buhari ke wa ECOWAS tare da shan awashin jawo hankulan manyan kungiyoyi da kasashe na duniya a kan batun matsalar kafewar ruwa a Tafkin Chadi.

A karshe ta nuna farin cikin ganin yadda Najeriya ta sake gyara ginin Majalisar Dinkin Duniya, wanda Boko Haram suka jefa wa bam a Abuja, cikin 2011.

Share.

game da Author