Jami’an Ofishin Babban Kwamishinan Kula da Masu Hijira na Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), sun ce masu gudun hijira sama da 90,000 da suka tsere daga Najeriya zuwa cikin yankin Kamaru, su na nan kalau, kuma a na kokarin dawo da su gida.
Wannan bayani ya fito har daga bakin jami’an gwnatin jihohin Adamawa da Barno, a jiya Litinin.
Wadanda suka yi hijirar dai akasarin su daga jihar Barno su ke, suk sun yi kaura ne saboda kashe-kashe da Boko Haram ke yawan yi musu.
A wata ganawa da aka yi a Yola, jihar Adamawa a jiya Litinin, Kwamishinan Yada Labarai, Ahmed Sajoh, ya ce ana shirin kwaso su daga sansanin Minawawo da ke cikin Maiduguri zuwa wani sansanin da za su fara yada zango a cikin Jihar Adamawa.
“Kusan 4,000 daga masu hijirar ‘yan Jihar Adamawa ne. Don haka an shirya wasu kauyuka sun amince za su karbi 1,500 daga na jihar Barno, wadanda suka nuna cewa sun amince su zauna a jihar Adamawa.” Inji Sajoh.
Kwamishinan dai bai fadi ranar da za a fara kwaso su ba, amma dai ya ce da jiragen sama za rika kwaso su daga kasar Kamaru.
Wakilin Jihar Barno a wurin taron, Kulima Kachalla, ya gode wa zumuncin da Jihar Adamawa ta nuna, sannan ya ce Barno za ta bada hadin kai wajen ganin aikin jigilar kwaso masu gudun hijirar ya yi nasara.