Alkalin Kotun Majistare a Kano ya bada odar kama ma’aikatan Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll.
Wadanda aka bada umarnin kamawar sun hada Mannir Sanusi da wasu ma’aikatan su biyu.
Mannir Sanusi dai shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Sarki.
Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci ce ta maka su kotu, inda ta kai karar Sanusi, wanda kuma shi ne Damburan na Kano.
Sauran sun hada da Mujitaba Abba da kuma Akanta na Masarautar Kano, Sani Muhammad-Kwaru.
Mai Shari’a Mohammed Idris ya bada umarnin a kama su saboda kin amsa kiran kai kan su ofishin hukumar hana cin hanci, domin su amsa tambayoyi bisa zargin kudade naira bilyan 4 da ake yi wa Mai Martaba Sarkin Kano.
Hukumar ce ta rubuta wa kotu takardar neman a kama su ukun.
Sammacen neman a kama su din wanda ke dauke da sa hannun Salisu Tahir, ya nuna cewa an bada umarnin kama su din bisa dokar kasa ta Sashe na 38.
Idan ba a manta ba, hukumar ta gayyaci mutane hudu, amma sai tsohon Sakataren Fadar Sarki, wato Isa Bayero da aka fi sani da Isa Pilot ne ya amsa gayyata.
Shugaban Hukumar Muhuyi Magaji ya ce wadanda aka ce a kama din dukkan su ana zargin su ne a binciken da ake yi.
Ya ce hukumar sa ta bai wa jami’an tsaro umarnin a kama su a duk inda suke.