Bayan Rantsuwa, Ba Zamu Sake Bawa Gwamnatin APC Uzuri Ba, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Duk abun da gwamnatin APC take so ta samu a wajen talakawan Najeriya ta samu.

Babu abun da talaka zai yiwa jam’iya mai mahimmanci da ya wuce ya zabeta a lokacin zabe.

Kowa ya ga yadda talakawa suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka zabi Buhari a mataki na farko a zaben 2015.

Sannan bayan kammala zango na farko cikin bayar da uzuri kala-kala, hakan bai sa talakawan sun kuma fitowa sun zabeshi duk da taron dangi da attajirai da yan siyasa suka yi masa.

Mustapha Soron Dinki

Mustapha Soron Dinki

Duk da cewa soyayyar tasa ta ‘dan ragu a zaben da ya gabata na 2019 duba da yadda alkaluman zaben ya nuna.

Farin jinin dan siyasa a zabe yake bayyanuwa, soyayyar tana bayyanuwa ne a akwatin zabe. Babu abun da yafi hakan mahimanci a wajen dan takarar siyasa.

Buhari bai samu masoya ba kamar na zaben 2015 saboda wasu daga cikin masoyansa sun yi fushi. Wasu kuma sun bar jam’iyar da su da iyayen gidansu tunda siyasar jogara ake yi a Najeriya musamman a Arewa.

Misali, kowa dai ya ga yadda aka kai ruwa rana da dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, wanda bai fi kuri’a miliyan hudu da dori Buhari ya bashi ba duk da cewa wasu ‘yan PDPn ma basu zabeshi ba.

Na tabbatar da hakan, saboda nayi ‘independent election observation’ a Kano. A karkashin kungiyar ‘The Youths-4-Change Network (The Y4CN).

To gaskiya, ita fa siyasa ribarta ta samar da gagarumin farin ciki a cikin mutane masu rinjaye. Kamar yadda John Stuat Mills ya fada. Ba a duba waye yake mulki, ana duba tasirinsa ga talakawan da suka zabeshi ne.

Saboda haka, duk uzurin da ‘yan Najeriya zasu bawa gwamnatin APC ya kare a wannan zangon mulkin na biyu. Domin Ita gwamnati a zahiri take (Reality). Duk kauyencin talaka zai iya ganin tasirinta a cikin rayuwarsa.

Mafi yawancin talakawa suna bukatar samun sauki, duk da cewa suna nan da soyayyar Buhari a ransu. Amma hakan baya nufin suna ganin daidai.

Yakamata gwamnati ta saka wa da talakawan nan da alheri don ganin ta samar da tasirinta a rayuwarsu kamar yadda kowa yake zaton zai faru idan Buhari yaci mulki.

Saboda babu lokaci, duk mulkin da yake da wa’adi yana bukatar gaggawa cikin tunanin abun da za a bayar da hujja (Reference) dashi a karshe.

Mun aminta, a waccen zangon, gwamnati tana cikin faduwar tattalin arziki da shirye shirye na yadda zata tinkari kasar.

Sai dai yanzu mun gode Allah, ko jiya NBS ta fitar da rahoton cewa Najeriya ta samu biliyan 289 daga haraji (VAT) a cikin watanni uku na farkon 2019. Gaskiya yakamata talakawa su ga shirin gwamnati a fili bayan dogon jira da suka yi.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author