Wasu da ba san ko su wane ba, sun barke sakareriyar jam’iyyar APC ta jihar Ogun, su ka sace takardun muhimman bayanai tare da sace kayayyakin da ke cikin sakateriyar.
Baya ga satar kayayyakin da suka yi masu tarin yawa, barayin sun kuma lalata wasu sassa na sakateriyar, domin hatta silin rufin ofisohin sai da suka yi wa kaca-kaca.
Kayayyakin da aka lalata wasu kuma aka sace, sun hada da takardun muhimman bayanai, A.C, talbijin da ilahirin ofisoshin, kujeru da dama a cikin sakatariyar.
Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Ogun, Derin Adebiyi ne ya sanar da haka a wani taron manema labarai a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Ya ce an fasa sakateriyar ne an kutsa ciki a ranar Laraba da tsakar dare.
Ya kara da cewa an shiga ofishin Sakataren Jam’iyya da na Sakataren Gudanarwa da sauran su.
Ya ce duk da dai ba a san dalilin da ya sa aka fasa sakateriyar ba, to akwai zargin wani abu a kasa, domin saura makonni biyu kacal wa’adin gwamna na yanzu, Adekunle Amosun ya kare.
Sannan kuma ya ce an rigaya an kai rahoto ga ’yan sanda. Kuma ya yi kira da cewa kowa ya kwantar da hankalin sa.