Sakamakon binciken da Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar ya nuna cewa an haifi jarirai bakwaini sama da miliyan 20 a duniya a shekarar 2015.
Sakamakon ya kara nuna cewa duk shekara duniya kan rasa kashi 80 bisa 100 daga cikin adadin yawan wadannan yara da ake haihuwa.
Sakamakon bincike ya nuna cewa akan haifi bakwaini miliyan 15 duk shekara a duniya inda daga ciki kashi 60 bisa 100 daga kasashen kudu da saharan Afrika suka fito.
Bakwaini sune jariran da ake haihuwa basu wuce wata bakwai a cikin uwayen su ba ko kuma sun wuce amma basu kai watanni tara ba da ake sa ran mace zata haihu ba.
Likitoci sun bayyana cewa mace kan haifi bakwaini a dalilin rashin kiyaye sharaddan inganta kiwon lafiya da wasu masu ciki basu yi.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Shugaban kungiyar ma’aikatan jinyar da suka kware wajen kula da yara kanana na Najeriya Olubunmi Lawal ta bayyana cewa Najeriya na cikin jerin kasashen duniya uku da suka fi fama da matsalolin haihuwar bakwaini.
Ta ce bincike ya nuna cewa kasar Sin itace kasar dake kan gaba wajen yawan jariran da ake haifa basukai watannin haihuwa ba sannan sai kasar India da ke bi mata. Najeriya ce ta uku cikin jerin kasashen da ake haihywar irin wadannan jarirai har 773,600 duk shekara.
Dalilai 6 dake sa a haifi da bakwaini:
1 . Zukar Taba Sigari
2. Mai dauke da Cutar siga (diabeties) ta Uwa ko ta uba.
3. Amfani da magungunan da wasu mata masu ciki ke yi batare da izinin likita ba.
4. Shan giya.
5. Rashin cin abincin da ya kamata.
6. Yawan rashin samun natsuwa da kwanciyar hankali ga mai ciki.
Discussion about this post