Sanata Ahmed Lawan da ke neman a zabe shi shugabancin Majalisar Dattawa, ya bayyana cewa idan aka zabe shi zai yi kyakkyawar mu’amala tsakanin majalisa da bangaren zartaswa na gwamnati.
Haka ya bayyana jiya Asabar a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai jiya Asabar a Abuja.
Lawan, wanda shi ne dan takarar da jam’iyyar APC da jiga-jigan ta, wanda Buhari ke goyon bayan ya zama shugaban majalisa, ya ce ya yi imani da cewa yawan samun sabani da sa-toka-sa-katsi tsakanin majalisa da bangaren gwamnati, ba alfanu ba ne, domin kasar ce da al’ummar da ke cikin ta abin ke rika shafa.
A yanzu dai shi ne Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa mai barin mulki cikin makon gobe.
Ya kara da cewa shekaru hudu da aka yi ana mulki tsakanin 2015 zuwa 2019, bangaren shugaban kasa bai samu kyakkyawar mu’amala da shuagabancin majalisar dattawa ba.
Ya ce a bangarorin biyu kowa ya sha kin amincewa a kan wasu batutuwa.
Sai dai kuma shi ya na da tabbatacin cea bai ga dalilin da zai rika sa-in-sa da bangaren gwamnati ba, matsawar dai kowa a tsaya a matsayin sa.
Ya ce mu’amala iri biyu ce tsakanin majalisa da bangaren mulki. Ko dai a yi kyakkyawa ko kuma a yi mai tsami.
Ya ce tabbas akwai inda bangaren gwamnati za su bijiro da wasu batutuwa masu kyau, amma majalisa kuma za ta yi musu duba da irin ta su fahimtar a bisa yadda doka ta shimfida komai.
Lawan ya ce ba zai yi ja-in-ja ko sa-in-sa da bangaren shugaban kasa ba. Sai dai ya kara da cewa ba kuma zai zama rakumi da akalar da za a rika jan sa sakaka ba.
Daga nan sai Lawan ya kara jinjina goyon bayan sa ga Shugaba Buhari da kuma Gwamnatin sa.
Kuma ya sha alwashin gudanar da komai a bisa amincewar mafiya rinjayen ‘yan majalisa.
Ya ce tabbas shi makusancin Buhari ne, kuma rikakken mai goyon bayan sa. Amma kada kuma jama’a su dauka cewa idan ya zama shugaban majalisar dattawa zai zama rakumi da akala ne kawai sai yadda aka yi da shi.
Cikin masu takara da Sanata Lawan har da Sanata Ali Ndume daga Jihar Barno da kuma Sanata Danjuma Goje daga Jihar Gombe.
Sanata Lawal ya fito ne daga jihar Yobe. Tun 1999 ya ke cikin bangaren adawa sai cikin 2015 ya samu kasancewa cikin jam’iyya mai mulki.
Discussion about this post