“Ba ka is aka daddatsa mana masarautu ba” – Bbong Gwom Jos ga Lalong

0

Mai martaba Gbong Gwom Jos, kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Filato, Jacob Buba Gyang, ya yi kurarin cewa Gwamnan Jihar Filato ba shi da ikon daddatsa masarautun jihar.

“Ni dai ban san ko akwai wani iko da gwamna ya ke da shi da zai iya shata wasu sabbin kan iyakokin masarautun gargajiya, matsawar babu wani tashin hankali ko matalar da za ta tilasta yin hakan.” Inji Buba.

Jiya Juma’a ne basaraken ya yi wannan furuci a Jos, babban birnin Jihar Filato a wurin taron shekara ta 2019, na Gangamin Bikin Al’adun Kabilar Birom.

Ya yi kalamin ne a matsayin martani dangane da wata sanarwa da Gwamnatin Jihar Filato ta fito da ita, inda ta kirkiro sabbin masarautu biyu daga Majalisar Masarautun Gargajiyar Jihar Filato.

Kirkiro masarautun Jos ta Arewa da Birom da aka yi, ya rage wa Gbong Gwom din karfi da yawan masarauta matuka.

Cire Birom da Jos ta Arewa da aka yi, ya bar Gbong Gwom da mulkin kananan hukumomi biyu rak, su ne Jos ta Kudu da Barkin Ladi.

Sanarwar da aka fitar ranar Alhamis ta nuna cewa basarake Attah na Ganawuri zai zama Sarkin Masarautar Birom, shi kuma Sarkin Anaguta da Afizere zai kasance rike da mukaman sarauta biyu a Jos ta Arewa.

Sai dai kuma Gbong Gwom na Jos, ya gargadi gwamna Lagong cewa sarautun gargajiya fa sun ma girmi Najeriya ita kan ta, kuma kowace kabila a Jihar Filato ta na da iyakar kasar ta.

“Don haka mu na kira ga ’yan siyasa su kiyaye da wadannan kan iyakokin masarautu.” Inji Gyang.

Ya ce akwai dokar kan iyakokin masarautun gargajiya shimfide a cikin kundin tsarin mulki. Don haka bai yiwuwa a zo da rana tsaka a yi wa dokar karan-tsaye.

Share.

game da Author