‘ Yan Afrika uku da ke wasa a Premier League na Ingila, Pierre Aubameyang, Mohamed Salah da Sadio Mane, sun lashe kyautar Gwarzon Cin Kwallayen Premier na 2018/2019.
Jiya Lahadi ce aka kammala gasar, inda kungiyar Manchester City ta samu nasarar cinye kofin, bayan ta tsere wa Liverpool da maki daya tal.
Dukkan wadannan ’yan wasa uku su na da kwallaye 22 kowanen su.
Salah da Mane sun a buga wa Liverpool, yayin da Aubameyang na wasa a Arsenal.
Wannan ne karo na farko da ’yan wasa uku suka yi kankankan a yawan cin kwallayen Premier, tun bayan gasar 1990/1989, inda Hosselbaink, Macheal Owen da Dwight Yorke suka yi kankankan.
Sannan kuma wannan ne karon farko da Aubameyang da Mane suka taba cin kyautar.
Salah ya lashe ne a karo na biyu, domin gasar bara ma shi ne ya yi nasara, shi kadai.