Kungiyar ‘Medical Guild’ reshen jihar Legas ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta karo ma’aikata a asibitocin dake jihar domin inganta kiwon lafiyar da mutane ke samu.
Shugaban Kungiyar Babajide Saheed yace rashin yin haka zai iya gurgunta ayyukan fannin kiwon lafiyar jihar ganin cewa dama can ana fama da wasu matsalolin.
” A yanzu haka likita daya a asibiti na aikin likitoci biyu ko kuma uku sannan albashin sa ba wani abin a zo a gani bane.
Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun koka kan yawan mutuwan yara da mata da ake ake fama da shi a Najeriya
Ma’aikatan kiwon lafiya ta fadi haka ne bisa ga rahotan yawan mutuwar yara da mata da kungiyar WHO, Asusun UNFPA da Asusun UNICEF suka bada a taron wayar da kan mutane game da illolin rashin samun ingantaccen kiwon lafiya da ya gudana a kwalejin koyar da aikin likitanci dake jihar Legas.
A jawabin ta babban bakuwa a taron Olusola Odujinrin ta ce har yanzu akwai sauran rina a kaba domin dole sai Najeriya ta maida hankali wajen inganta fannin kiwon lafiyar kasar ba za a kai ga nasara ba.
Ta kuma kara da cewa rahotan ya nuna cewa Najeriya na samun karin akalla kashi 15 bisa 100 na yawan mutuwan da ake samu a kasar amma tace hakan zai iya zama labari idan aka mai da hankali wajen kau da matsalolin da ya addabi fannin kiwon lafiyar kasar.
Bayan haka Odujinrin ta ce daya daga cikin matsalolin da ke gurgunta fannin kiwon lafiya musamman cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko shine karancin kudi.
” Har yanzu ana matukar fama da rashin kudi a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko, wanda hakan yakan sa kaga hatta kayan aiki a asibitocin sun kare babu ko allura.”
Discussion about this post