An yi garkuwa da masu dafa abinci hudu a makarantar mata dake Zamfara

0

A yau Alhamis ne kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Celestine Okoye ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da masu dafa abinci hudu a makarantar sakandare na mata dake kauyen Moriki a karamar hukumar Zurmi jihar Zamfara.

Okoye ya ce masu garkuwa da mutanen sun far wa wannan makaranta ne ranar Laraba.

” Masu garkuwa da mutane sun sace masu dafawa dalibai abinci su hudu a makarantar bayan sun datse hanyar shiga.

Okoye ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin ceto wadannan mutane da aka sace.

Sai dai duk wannan bayanin da Okoye ya yi wasu kafafen yanar giso da wasu gidajen jaridu kamar BBC Hausa sun ruwaito cewa masu garkuwa da mutanen sun sace malamai biyu ne da masu dafa abinci hudu a makarantar.

Idan ba a manta ba a jiya Laraba ne Masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da mutane 16 a kauyen Zurmi jihar Zamfara suka bukaci lalle a biya su Naira miliyan biyar kudin fansa kafin su saki mutanen dake tsare a wajen su.

A hirar da suka yi da maharan ta wayar tarho shugaban kungiyar ya bayyana cewa Naira miliyan 3.5 din da aka biya a matsayin kudin fansa da farko ya zama lada inda ya yanzu haka suna bukata a sake biya su Naira miliyan biyar kafin su saki mutane 16 da suka kama.

Masu garkuwa da mutanen sun sace mutane 16 daga wannan kauye a ranar 29 ga watan Janairu.

Share.

game da Author