An yi garkuwa da dan NYSC da wani fasto a Barno

0

Hukumar Jin dadin Masu Aikin Bautar Kasa (NYSC)na jihar Barno ta sanar cewa Boko Haram ta yi garkuwa da wani dake bautar kasar sa a jihar tare da wani faston cocin ‘Living Faith’.

Jami’in NYSC Rabi’u Aminu ya sanar da haka wa manema labarai ranar Litini a Maiduguri.

Aminu yace Boko Haram sun yi garkuwa da Abraham Amuta mai lambar rajista BO18b/067 da faston cocin ‘Living Faith’ mai suna Oyeleke a hanyar zuwa garin Chibok daga Maiduguri ranar 10 ga watan Afrilu.

” Tun da wannan abu ya faru muka kasa samun kwanciyar hankali musamman yadda bincike ya nuna mana cewa Amuta ya yi tafiyar sa ne batare da ya nemi izinin NYSC ba.

” A jihar Barno NYSC na aikawa da masu yi wa kasa hidima kananan hukumomi hudu kadai daga cikin kananan hukumomi 27 dake jihar.

” Wadannan kananan hukumomin sun hada da Jere, Bayo, Biu da Maiduguri Metropolitan Council (MMC) sannan domin guje wa irin haka ne muka kafa dokar neman izini kafin wani dan NYSC ya yi tafiya koda za shi.

A karshe kwamishinan ‘yan sandan jihar ya tabbatar musu da goyan bayan rundunar wajen ganin an cewo Amuta daga hannun Boko Haram.

” Muna kuma kira ga mutane da su taya mu da adu’o’I domin Allah ya sa a gano Amuta.”

Share.

game da Author