An tsinci gawar wani sojan ruwa a cikin dakin sa a makarantar manyan sojoji dake jaji.
Shi dai wannan Soja daya ne daga cikin sojojin da zasu yi tafiya kasashen Afrika ranar Lahadi.
Rashin ganin sa da abokanan tafiyar sa ba su yi ba ya sa suka farga in da aka fantsama neman sa.
Ko da aka kai ga dakin sa sai aka ganshi kwance a ciki sharaf cikin jini sannan ga shirgegen dutse nan a gefan sa.
Daga nan dai aka fito da gawar sa da ake ganin kamar ya fara rubewa ma.
Binciken gaggawa da aka yi ya nuna cewa akwai yiwuwar cewa ya mutu tun ranar juma’a ne.
Kakakin rundunar sojojin Ruwa Suleiman Duhu ya bayyanawa wakilin mu ta wayan tarho cewa ba shi da masaniya game da mutuwar wannan soja.
PREMIUM TIMES ba za ta fadi sunan sojan ba tukuna domin ba mahukunta damar ganawa da iyalan wannan mamaci