An kona gidaje 12, mutane biyar sun mutu a rikicin Filato

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta bayyana cewa mutane biyar sun mutu sannan an kona gidaje 12 a rikicin da ya kaure ranar Lahadi a jihar.

Kakakin ‘yan sanda Tyopev Terna ya sanar da haka wa manema labarai ranar Litini.

Terna yace rikicin ya auku ne a garuruwan Dutse Uku da Unguwan Damisa dake karamar hukumar Jos ta arewa ranar Lahadi a dalilin tsintar gawar wani matashi mai suna Enoch Monday.

Terna yace kafin rikicin ya barke wani mazaunin kauyen Tina mai suna Sarki Arum ‘m’ ya kai kara ofishin su cewa sun tsinci gawar wannan matashi.

” Jin haka sai muka gaggauta dauke gawar amma kafin mu Ankara labarin mutuwar Monday ya kareda kauyukan inda matasan kauyukan suka fara zanga-zanga.

” Rikicin dai ya yi sanadiyyar rayukan mutane biyar sannan an kona gidajen 12 a dalilin wannan zanga-zanga da matasan suka yi.

Terna yace rundunar tare da hadin guiwar sauran jami’an tsaro a jihar sun tsayar da wannan rikici kuma an samar da tsaro a wannan unguwanni.

Share.

game da Author