Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta bayyana cewa ta kama masu aikata miyagun aiyukka 26 wanda a ciki akwai wani malamin almajirai.
Kwamishinan ‘yan sanda Ibrahim Kaoje ya sanar da haka dayake zantawa da manema labarai ranan Litini a garin Sokoto.
Ya ce sun kama wadannan mutane a tsakanin ranakun 24 zuwa 26 ga watan Mayu.
” Laifukan da wadannan mutane suka aikata sun hada da kwana da maza wata luwadi,fashi da makami, harkallar miyagun kwayoyi, kisa da sauran su.
Kaoje yace sun fara kama wani malamin almajirai mai suna Murtala Maude da laifin yin lalata da daliban sa maza har su 10.
” Maude na koyar da dalibai 60 a makarantar sa dake Arkilla Magaji.
Kaoje yace bayan haka sun kama wasu Hali Custom da Muhammad Dan’yamai da laifin siyar da tabar wiwi.
Ya ce sun kuma kama wasu ‘yan bata gari 12 dauke da makamai da ya hada da adduna da wukake.
” Mun kuma kama Zakariyya Sani, Umar Hassan da Hamza Sama’ila da laifin fasa shaguna mutane.
” Kayan da muka kama su da su za su kai na Naira miliyan 4.5 sannan biyu daga cikinsu sun tabbatar mana cewa sune suke aikata fashe-fashen shaguna a unguwannin su.
Bayan haka Kaoje yace rundunar ta kama Ali Ukawa da Musa Bajini da laifin daukan makamai sannan da kishe wani Alhaji Katu dake zama a kauyenMaikaza a karamar hukumar Goronyo.
Ya ce sun kuma kama wasu ‘yan banga da aka fi sani da ‘yan sakai’ guda shida da laifin kashe wani Muhammadu Kadade dake zama a kauyen Jigawa a karamar hukumar Kebbe.
Kaoje yace rundunar ta kammala yin bincike a kan wadannan mutane sannan za ta maka su a kotu domin yanke musu hukunci.