An kama gungun masu garkuwa tare da sojan da ke jagoran su –’Yan sanda

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta sanar da kama wanin gugun mutane hudu da suka addabi jama’a su na yin garkuwa da su.

Wadanda aka kama din kan rika sanya kayan sojoji domin yaudarar jama’a su na yin garkuwa da su.

Daga cikin su hudun, akwai soja daya mai mukamin Lance Corporal, wanda ke sanye da kayan sa na sojoji a lokacin da aka kama su a ranar Juma’a.

An samu nasarar kamas bayan sun yi garkuwa da wani mai suna Uchenna Ezeonu a garin Ekwulobia, Jihar Anambra.

Kakakin ’Yan Sandan Anambra, Haruna Mohammed, ya kara da cewa an cewo wanda aka yi garkuwar da shi tun kafin a ce an yi masa wani lahani.

Wadanda aka kama din sun hada da Obasi Peter, Benjamin Nicholas da Ojiegbe Obinna. An kama su tare da sojan guda daya.

An kama su ne a kan hanyar Isoufia a Aguata bayan sun yi garkuwa da Ezeounu.

Ojiegbe Obinna shi ne aka samu sanye da kayan sojoji, Obasi da Nicholas kuma sanye da singiletin sojoji.

Yayin da ake ci gaba da bincike, ‘yan sanda sun gano cewa Lance Corporal Obinna ya na aiki ne karkashin Bataliya ta Musamman ta 101 da ke Maiduguri, Jihar Barno.

An damka shi a hannun sojojin Rundunar Onitsha, yayin da sauran biyu din kuma aka gano sojojin bogin ne.

Share.

game da Author