An gayyaci Buhari wani taro a kasar Faransa

0

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya gayyaci Shugaba Muhammadu Buhari taro da za a yi a kasar tsakanin Faransa da kasashen Afrika.

Za a yi taron cikin watan Yuni, 2020 a birnin Bordeaux na Faransa.

Babban Sakataren Taron Afrika da kasar Faransa, Stephanie Rivoal ce ta bayyana haka a lokacin da ta kai ziyara ofishin Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama a jiya Talata, a Abuja.

Ta ce taron za a tattauna ne domin samo hanyoyin da za a shawo kan matsalar kauyuka ke fuskanta har suke yawan kwarar birane, can ma birane na kara samun matsalar cinkoso a fadin Afrika.

Ta ce ta na fatan Buhari da Macron za su halarta domin muhimmancin da taron ke da shi.

Ta ce ana kyautata zaton taron zai samar da sahihiya kuma intangacciyar hanyar shawo kan matsalar da cinkoron biranen Afrika da mac wasu matsalolin da biranen ke fuskanta.

Ta kara da cewa a wurin taron, ministocin kasashe daban-daban za su zauna su tattauna da junan su, inda kowane zai bayyana irin nasarar da ya samu wajen ci gaban birane, kuma a fitar da matsalolin da sauran birane ke fuskanta tare da hanyoyin magance su.

Share.

game da Author