Ma’aikatar kiwon lafiya na kasar Singapore ta gano cutar ‘Monkey Pox’ a jikin wani dan Najeriya mai shekaru 38 da ya shigo kasar.
Sakamakon binciken da ma’aikatar ta gudanar ya nuna cewa wannan mutum ya kan yi muamula da nama daji a lokacin da yake Najeriya sannan s daidai zai taho kasar Singapore din ya cicci naman daji da ake kyautata zaton anan ne ya kamu.
A yanzu haka wannan mutum na kebe a wani bangare a asibiti a na duba shi.
Ma’aikatar ta kuma fara duba mutane 23 da suka yi muamula da wannan mutumi domin kada cutar ta yadu.
A kwanakin baya Hukumar kula da kiwon lafiya ta kasar Britaniya (PHE) ta sanar cewa an gano cutar Monkey Pox a jikin wasu ‘yan Najeriya biyu a kasar.
A dalilin haka shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa hukumar za ta hada hannu da hukumar PHE don ganin an tarerayi cutar kafin ta yadu.
Shugaban hukumar PHE Nick Phin ya bayyyana cewa an fara gano wannan cuta ce a jikin wani dan Najeriya a makon da ya gabata a asibitin ‘Cornwall’ sannan wannan makon ne aka gano na biyu din a asibitin ‘Blackpool Victoria’.
Phin yace bisa bincike cutar Monkey Pox ya bullo a Najeriya tun a shekarar 2017 sannan zuwa Agustan 2018 mutanen da suka kamu sun kai 262 a jihohi na kasar nan.
Ya ce binciken ya kara nuna cewa mutane 113 daga jihohi 16 sun rasu a dalilin kamuwa da cutar.
A karshe Ihekweazu ya ce NCDC za ta hada karfi fa karfe da kungiyar WHO, UNICEF da sauran kungiyoyin domin kawar da cutar a Najeriya.