Hukumar Hana Ma’aikatan Gwamnati Cin Rashawa, ICPC, ta bayyana cewa an daure tsohon Shugaban Hukumar Gudanarwa na Babbar Kwalejin Fasaha ta Jihar Kwara, Alanamu a gidan kurkuku saboda laifin rashawa.
An daure shi tare da Salman Sulaiman, Babban Darakta na kamfanin Namylas Nig. Ltd, saboda laifin karba da bayar da cin hanci.
Tun farko dai an gurfanar da su ne a gaban Mai Shari’a Abdulgafar na Babbar Kotun Jihar Kwara da ke Ilorin, bisa tuhume-tuhume guda takwas da suka kunshi karba da bayar da rashawa.
An ki amsa laifin su, kamar yadda ICPC ta bayyana.
Idan ba a manta ba, an zabi Alanamu a matsayin mamba a Hukumar ICPC a cikin 2017, amma daga baya aka cire sunan sa, saboda zargin cin rashawa, wanda hukumar ta yi bincike.
An kama shi da laifin karbar cin hancin naira milyan 5 daga wani dan kwangila wanda abokin sa ne, a matsayin kashe-mu-raba daga wata kwangila da aka bayar.
Shi kuwa Sulaiman, an zarge shi ne da laifin bayar da cin hanci ko toshiyar baki ga jami’in gwamnati, wanda ya bai wa Alanamu ta hanyar zuba masa kudaden a asusun san a GTB.
An ce ya bada kudin ne a matsayin tukuicin bayar da kwangila ga kamfanin da da aka yi.
Lauyan ICPC ya ce Sulaiman ya bayar da takardun bayanai na karya a lokacin da ya nemi a bai wa kafanin sa Namylas Ltd kwangilar.
Sannan kuma kotu ta tabbatar da cewa Alanamu ya bayar da kwangilar ta gina babban dakin taro a Kwalejin Fasaha akan kudi naira milyan 182, ga kamfanin abokin sa, alhali kuma bai cancanta ba.
An yanke wa Alanamu hukuncin biyan naira milyan 25 kuma an daure shi shekara biyar.
Shi ma Sulaiman an daure shi shekara bakwai tare da tarar naira milyan 1 daya.