Kwamishinan Zabe na INEC na Jihar Kwara, Garba Madami, ya yi ikirarin cewa ya ki karbar kudin da aka nemi a ba shi domin ya karkatar da sakamakon zaben da aka kammala na 2019 a jihar.
Madami wanda wanda dan asalin Karamar Hukumar Gurara ne, ya yi wannan bayani ga manema labarai jim kadan bayan kammala daurin auren ’yar sa a Minna, babban birnin Jihar Neja.
“Na sha fama da matsin-lamba daga wajen ’yan siyasa, wadanda suka rika nuna za su ba ni kudi domin na karkatar da zaben 2019 a Jihar Kwara, amma na tsaya kai-da-fata, na ce ban yarda a yi magudi ba.” Inji shi.
Madami ya ce yanayin irin aikin su a INEC ya na da hatsari sosai, domin za a rika ribbatar jami’in INEC da kudade. Amma babban hatsarin shi ne jami’i ya karbi kudin.
“Wannan kuma ya rage tsakanin ka da Allah ka yi abin da ya dace, wanda yin hakan zai kare maka kima da mutunci da darajar ka. Ko kuma ka zubar da mutuncin ka ka karba, a karshe kuma a daure ka a kurkuku.
Daga nan ya yi tir da siyasar kudi, wadda ya ce su ’yan siyasa a tunanin su,don suna da kudi, to za su iya sayen mutuncin kowa.
“Abin da na yi a jihar Kwara tun kafin zabe, shi ne sai na shiga gidan radiyo na shaida cewa babu wani tulin yawan kudin da za su iya bude min idanu, har a ce an saye ni domin na yi wa wata jam’iyya rashin adalci.”
A karshe ya ce yawan kararrakin da ke gaban shari’a daga zaben 2019, ba wani abu ba ne, sai kawai rashin alkibtar da jam’iyyun siyasa da ’yan siyasa ba su da shi.
Ya ce da kowace jam’iyya za ta bi sharuddan da aka gindaya, to watakila ma da ba a samu yawan kararrakin har 765 a gaban kotunan sauraren kararrakin zabe ba.
Discussion about this post