Amfani 10 da ‘Graviola’ ko kuma ‘Tuwon Biri’ ke yi ga kiwon lafiyar mutum

0

Bayanai sun nuna cewa manoma a kasar Mexico ne suke noma ta a duniya amma a dalilin gano sinadarorin inganta kiwon lafiya da yake dauke da shi ya yadu zuwa kasashe dabam-dabam na duniya.

A Najeriya Yarbawa na kiran sa Ebo ko kuma Apekan, da Hausa kuma tuwon biri sannan da turanci soursop ko kuma Graviola.

Masanan wannan itace sun bayyana cewa daga bishiyar har zuwa ganye da rassanta na dauke da sinadarorin da zai inganta kiwon lafiyar mutum.

Likotoci sun tabbatar da cewa tuwan biri na maganin cutar daji da kuma kare mutum daga kamuwa da wasu cututtuka.

Ga amfanin Tuwon Biri

1. Yana warkar da cutar siga wato ‘Diabetes’

2. Yana warkar da cutar huhu.

3. Shan ruwan gayan Tuwan biri na taimakawa masu kasa iya barci samun barci.

4. Yana warkar da basir.

5. Yana maganin mura.

6. Yana warkar da cutar daji musamman wanda ke kama dubura, nono,’ya’yan maraina, huhu da makogwaro.

7. Yana rage hawan jini.

8. Yana dauke da sinadarin Vitamin C wanda ke taimakawa wajen warkar da ciwo ko rauni.

9. Yana dauke da sinadarin Vitamin B1.

10. Sannan yana taimakawa wajen nika abinci da kara karfi a jiki.

Share.

game da Author