Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa lallai akwai yiwuwar zai ci gaba da aiki da wasu daga cikin ministocin sa a wannan zangon.
Buhari ya ce kowani minista ya rubuto sakamakon ayyukan da yayi da irin nasarorin da ya samu. Sannan ya mika takarda bankwana ga sakataren gwamnatin tarayya.
Sai dai kuma a hira da yayi da gidan talabijin din NTA, Buhari ya shaida cewa wannan karon fa kowa sai ya tashi tsaye musamman fannin shari’a da tsaro. ya ce ba zai yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda yake wa sda aikin sa musamman a wadannan fanni biyu.
Ya ce duk wanda aka samu yana wa ayyukan wadannan fanni zagon kasa zai kuka da kan sa.