Shugaban Riko na Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya yi zargin cewa akwai wasu gwamnonin jihohin kasar nan da ke fakewa da karya ko gaskiyar matsalar tsaro su na sace makudan kudaden jama’a.
Magu ya yi wannan bayini ne a yayin da ya ke jawabi a kan cin hanci da rashawa a wurin taron Sanin Makamar Aikin Zababbun Gwamnoni, a Abuja.
Ya ce yanayin matsalar tsaro da kuma ta’addanci sun kara hauhawar cin hanci da rashawa, ta yadda wasu gwamnonin jihohi ke wawurar kudade salum-alum.
“…Har tulin hujjoji gare mu, wadanda ke tabbatar da yadda wasu gwamnonin jihohi ke kwashe kudade ta hanyar amfani da dalilai na matsalar tsaro.
“Kai a na ma rade-radin cewa wasu gwamnonin kiri-kiri su ke kara rura wutar matsalar tsaro a jihohin su, domin su kara yawan tulin kudaden da suke warewa kan matsalar tsaro.
“Ba sai ma na shiga na yi nisa a batun kwasar kudi da sunan matsalar tsaro ba. abu mafi muhimmanci dai shi ne gwamnoni su yi taka-tsantsan wajen kashe kudaden jama’a. Kuma duk abin da za su yi, su guji harkalla da kumbiya-kumbiya. Su yi komai kan ka’ida kuma a sarari.”
Shi ma Nuhu Ribadu, Shugaban hukumar EFCC na farko, ya ja hankulan zababbun gwamnoni da su guji yin wala-wala da kudaden jama’a, ciki har da kudaden tsaro da ake ware musu a duk wata.
Ribadu ya ce kudaden al’umma ana bada su ne domin a yi musu ayyukan more rayuwa, ko saukaka kuncin rayuwa. Ba wai kudi ne da aka amince kowane gwamna ya rika rafkewa kamar kudin da ya gadaba.