Akalla yara 11,000 ne ke kamuwa da tarin fuka a duk rana a duniya a dalilin shakar hayaki – Bincike

0

A wani bincike da aka yi daga jami’ar George Washington DC kasar Amurka an gano cewa shakar gurbataccen iska musamman na hayakin ababen hawa na yin sanadiyyar kamuwar tarin fuka da yara kan yi fama da shi.

Masu binciken sun gudanar da binciken ne a manyan birane 125 dake kasashe 195 a duniya.

Sakamakon binciken ya nuna cewa yaran dake zama a cikin birare da wadanda ke zama a wuraren da ababen hawa suka yi yawa sun fi kamuwa da tarin fuka.

Akan kamu da tarin fuka ne idan aka yawaita shakan hayakin dake fitowa daga motoci da babura.

Binciken ya kuma nuna cewa duk rana yara 11,000 ne ke kamuwa da wannan cuta a dalilin shakar irin wannan iska a fadin duniya.

Shakar irin wannan iska na kawo cututtuka kamar su dajin dake kama huhu, shanyewar bangaren jiki, cututtukan dake kama zuciya da sauran su sannan adadin mutanen dake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar sun kai a kalla kashi daya bisa uku na yawan wadanda suka kamu a duniya.

WHO ta bayyana cewa aiyukkan goma, masana’antu, makamashi, hayakin ababen hawa, hayakin risho, tara bola na cikin abubuwan dake gurbata iska sannan hakan na kawo canjin yanayin dake cutar da kiwon lafiyar mutane.

Kungiyar WHO ta ce domin shawo kan wannan matsalar ne za ta shirya taro domin daukan matakan da ya kamata abi don kawo karshen haka.

Share.

game da Author