AIKIN KWASTAN: Mutane 524,315 na neman aikin guraben ma’aikata 3,200

0

Hukumar Kula da Aikin Kwastan ta Kasa ta sanar da cewa masu neman aiki har su 524,315 ne ke neman aikin gurabe 3,200 da suka sanar za a dauka.

Sanarwar ta kara da cewa har mutane 828,333 suka cika fam a intanet na neman aikin. To amma dai ya zuwa yau, 524,315 suka kammala cika fam din na su.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kwastan, David Attah ne ya sanar da haka a lokacin da ya ke zanta wa da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), Jiya Litinin a Abuja.

A ranar 17 Ga Afrilu ne Hukumar Kwastan ta sanar da cewa ta bude shafin cika fam na neman aiki a intanet, inda za ta dauki sabbin ma’aikta 3,200.

Za a dauki manyan jami’ai 800, wato Sufurtanda sai kuma kanana masu mukamin Sufeto na Kawastan da kuma Mataimakin Kwastan su 2,400.
Attah ya kara da cewa mutane 278 suka cika fam na neman Sufurtanda, yayin da saukan kuma duk mukaman Sufeto da Mataimaki suka cika.

Ya jaddada cewa Hukumar Kwastan za ta yi amfani da cancanta, adalci da kuma gaskiya, ba tare da nuna bambanci, bangaranci ko nuna sanayya ba.

Share.

game da Author